ABNA24 : A wani bayyaninsa da aka watsa a gidan talabijin din kasar, Shugaba Rauhani, ya ce ci gaba da matsin lambar da Amurka ke yi wa Iran, ta fuskar siyasa da shari’a, sun mayar da Amurkar saniyar ware.
Wannan dai na zuwa ne bayan da manyan kasashen duniya sukayi watsi da sanarwar da Amurka ta bayar na cewa an dawo da takunkuman MDD, kan kasar ta Iran.
A sanarwar ba-zata data fitar, Amurka ta yi gaban kanta wajen sanar da sake kakabawa Iran dukkanin takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakaba mata a shekarun baya, wadanda daga bisani majalisar dinkin duniya ta janye su bayan cimma yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran a shekarar 2015.
342/